Tarihin Marigayi Sarkin Bauchi Alh. (Dr) Sulaiman Adamu

Alhaji Sulaiman Adamu ya rasu a ranar 23 ga watan Yuli shekarar 2010 a wani asibiti dake Masirah 
Marigayi Sarkin Bauchi Alh (Dr) Sulaiman Adamu. Sarkin Bauchi na 10.
An haifi Marigayi Sarkin Bauchi Alhaji Sulaiman Adamu ne a ranar 7 ga watan Janairun 1933 a garin Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya. Marigayin ya halarci makarantar Firamare ta Kobi daga shekarar 1946 zuwa 1948.
Daga nan an saka shi a makarantar Midil ta Bauchi daga shekarar 1948 zuwa 1949, kafin ya zarce zuwa kwalejin Barewa da ke Zariya tsakanin shekarar 1950 zuwa 1954. Kafin daga bisani ya halarci kwalejin kimiya ta Torquay a Devon ta Ingila tsakanin shekarar 1961 zuwa 1962, inda ya samu takardar shedar Diploma akan harkokin mulki.
Marigayi Sarkin Bauchi Sulaiman yayi aiyuka da dama da suka haɗa da mataimakin Injiniya daga shekarar 1954 zuwa 1956. Hakimin Gwana daga shekarar 1960 zuwa 1963. Ya zama hakimin Bauchi daga shekarar 1963 zuwa 1968, sai kuma ya zama Hakimin Galambi daga shekarar 1968 zuwa 1971.
Daga shekarar 1971 Marigayi Sarkin na Bauchi ya fara aiki da gwamnatin tarayya, inda ya zama jami'in hada-hadar baƙi a ma'aikatar harkokin waje. Tsakanin shekarun 1971 zuwa 1982 ya zama sakatare a ofishin jakadancin Najeriya da ke Masar, sai kuma ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva a matsayin sakatare mai lura da harkokin siyasa tsakanin shekarar 1976 zuwa 1978.
Haka kuma ya zauna a ofisoshin jakadancin Najeriya dake Burkina Faso ya kuma zama babban jami'i mai lura da fasfo tsakanin shekarar 1979 zuwa 1982. Marigayi Sarkin Bauchi Sulaiman Adamu ya zama Sarkin Bauchi na 10 a ranar 27 ga julin 1982. Ya kuma zama shugaban jami'ar kimiyya da fasaha dake Anambra tsakanin shekarar 1984 zuwa 1987. Kafin rasuwarsa ya samu kyautar lambar yabo ta CFR da kuma digirin girmamawa ta LLB.
Alhaji Sulaiman Adamu ya rasu a ranar 23 ga watan Yuli shekarar 2010 a wani asibiti dake Masar. Ya rasu ya bar matan aure huɗu da 'ya'ya 19. Kuma ɗaya daga cikin 'ya'yan sa Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ɗan shekaru 40 ne ya gaje shi, inda ya zama Sarkin Bauchi na 11.
Next
Newer Post
Previous
This is the last post.

Post a Comment

 
go to the Top